Tun bayan da wasu faya-fayen bidiyo su ka bullo masu nuna Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na karbar wasu kudade da aka ce cin hanci ne, jama'ar ciki da wajen jahar su ka shiga takaddama kan sahihancin faya-fayen bidiyon ko akasin haka.
Wasu daga cikin faya-fayen bidiyon na nuna kamar Gwamnan Ganduje na karba da kuma saka makudan kudaden cikin ambulan da kuma aljuhu, bayan ya karbo daga wadanda aka ce wai 'yan kwangila ne.
Yayin da wasu ke ganin faya-fayen bidiyon sahihai ne, wasu kuma na ganin an yi dabara ce ta fasahar zamani aka hada faya-fayen, wadda jaridar Daily Nigeria ta wallafa.
Tuni dai gwamnatin Kano, ta bakin Kwanishinan Yada Labarun jahar, Mohammed Garba, ta ce za ta ruga kotu a bi kadi a shari'ance.
A halin da aka ciki kuma, a cewar wakilinmu, "Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta kafa kwamitin bincike game da wannan batu mai wakilai 7, wanda zai mika rahotansa ga zauren majalisar cikin makonni hudu masu zuwa."
Ga wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5