Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari, na neman amincewar Majalisar Dattawan kasar domin ya ciwo bashin dalar Amurka miliyan dubu dari biyar da rabi, ($5.5bn).
Sai dai wannan yunkurin ya sa wasu hukumomin kasa da kasa da jama’ar kasar jan kunnuwan shugabannin na Nigeria game da bashin. Su kansu ‘yan kasar kawunansu sun rabu akan lamarin.
Shugabannin Bankin Duniya, da Hukumar Bada Lamuni Ta Duniya ta IMF, sun gargadi Najeriya da tayi taka-tsantsan kan ciwo bashin.
Malam Sha’aibu Idris, wani kwararre akan sha’anin tattalin arziki, ya ce akwai alfanun cin bashi da kuma rashin alfanunsa. A cewarsa, basussukkan dake kan Najeriya da ta ciwo daga hanyoyi daban daban a can baya, sun yi yawa,saboda haka bai ga dalilin da kasar zata ci wani sabon bashin ba.
Amma Malam Ahmed Yusuf, tsohon babban daraktan Bankin Unity dake Abuja, ya ce cin bashin na da mahimmanci kuma zai yi tasiri saboda gwamnatin zata yi anfani da bashin ne wajen gina abubuwan da zasu taimakawa habakar tattalin arzikin kasa.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5