Shin Annobar Coronavirus Za Ta Iya Shafar Zaben 2020 a Nijar?

Hedikwatar Hukumar Zaben Nijar CENI

Mako daya bayan kammala rijistar zabe a Jamhuriyar Nijer, hukumar zabe ta CENI ta fara nuna shakku game da yiyuwar ayyukan rajistar ‘yan kasar mazauna kasashen waje, sanadiyar annobar coronavirus.

Shugaban hukumar zabe ta CENI Me Issaka Sounna ya sanar cewa, har yanzu ba a tsayar da ranar soma rajistar ‘yan Nijer mazauna ketare ba, sakamakon annobar coronavirus, yayin da lokacin gudanar da zabe ke karatowa.

Ya bayyana hakan ne a taron majalisar warware rigingimun siyasa wato CNDP da ya tattaro wakilan jam’iyyu na bangaren masu rinjaye da mambobin gwamnatin Nijer a karshen mako.

Tsarin jadawalin hukumar CENI ya yi nuni da cewa a watan Nuwamba 2020 ya kamata a gudanar da zaben kananan hukumomi, sai dai a yayin wannan zama hukumar ta nuna alamar ba za a samu gudanar da zaben ba.

Lamarin dai ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a wajen ‘yan siyasa a cewar shugaban jama’iyyar PNPL Akal kasa ta bangare masu mulki.

Jam’iyyar adawa wacce tun fil azal ke kallon hukumar ta CENI a matsayin haramtacciya ba ta halarci taron ba.

Ka-ce-na-ce akan tsare-tsaren zabe wani salo ne da ‘yan hamayya na yau ke amfani da shi don haddasa tarnaki in ji Assoumana Mahamadou wani jigo a jam’iyar PNDS mai mulki.

Zabe ‘yanci ne da kundin tsarin mulkin Nijer ya yi tanadi domin ‘yan kasa na ciki da waje, sannan kuma shirya zabe kafin wucewar wa’adin gwamnati mai ci shi ma wani abu ne da kundin tsarin mulki ya wajabta.

Saboda haka Firam Minista Birgi Rafini a karshen taron ya jaddadawa ‘yan kasar cewa za a gudabar da zabukan gama gari a watannin Nuwamba da Disamba 2020 ba fashi.

A ranar 2 ga watan Afrilun 2021, shugaba kasar Nijar Issouhou Mahamadou zai yi ban-kwana na cika wa’adinsa, sannan ya damka ragamar mulki a hannun wani sabon zabeben shugaban kasa.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.