Shigowa da Shinkafa Koma Baya Ne ga Manomanta a Najeriya - 'Yan Majalisa

Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Makon yija ne sabon shugaban hukumar kwastan Kanar Hamidu Ali mai ritaya ya sanarda da cire shinkafa daga jerin kayan abinci da gwamnatin tarayya ta hana shigo dasu.

Matakin da Kanar Ali ya dauka yanzu ya amince da shigowa da shinkafa kasar daga kasashen waje.

Wannan matakin bai yiwa 'yan majalisar wakilan Najeriya dadi ba. Onarebul Ibrahim Usman Auyo dake wakiltar mazabar Hadeija da Auyo da Kafin Hausa a majalisar tarayyar Najeriya yace matakin koma baya ne ga manoma shinkafa cikin Najeriya kuma ba zai haifar da da mai ido ba ga talakan kasa..

Yace Hadeija-Jama'are ta shafi kusan jihohi hudu duk suna noman shinkafa. Yace rashin inganta aikin noman shinkafa da ingantata ya sa manoman basa samun riba. Yanzu kuma da za'a kwararota daga waje ke nan an karya manomanta. Indan gwamnatin tarayya ta inganta noman shinkafa Najeriya zata ciyar da kanta da sauran kasashen dake makwaftaka da ita.

Shi ma Onarebul Rabiu Garba Kaugama daga jihar Jigawa cewa ya yi Kanar Hamidu Ali ya wuce gona da iri domin dokar hana shigo da shinkafa daga kasashen waje doka ce ta majalisar tarayya. Kamata ya yi ya tuntubi majalisar. Mutum daya ba zai iya ture dokar majalisa ba. Majalisar ta aiwatar da dokar ce saboda inganta manomanta da kuma kare kawo wasu cututuka kasar. Matakin da shugaban hukumar kwastan ya dauka na gurgunta manoman kasar ne.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shigowa da Shinkafa Koma Baya Ne ga Manomanta a Najeriya - 'Yan Majalisa