Shigowa Da Motoci: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Shugaban Kwastam

Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta gayyaci shugaban hukumar Kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya, domin yayi mata bayanin dalilan da suka sa aka fara amfani da dokar hana shigowa da motoci ta iyakokin Najeriya bayan Majalisar ta ce a dakatar.

Kungiyar masu sayar da motoci ta Najeriya ta nuna damuwa ga yadda matakin hana shigowa da motoci ta kan iyakokin ‘kasa, da hakan yanzu haka ya janyo musu babbar asara da kuma barazana ga karayar jarin wasu daga cikin su.

Yanzu haka akwai motoci da yawa da suka makale a kasashen waje da ‘yan kungiyar suka makara wajen shigowa da su har wa’adin dakatarwar ya cika. Shugaban kungiyar ta ‘kasa Prince Ajibola Adedoyin, yace basa hamayya da dokar kai tsaye, sai dai suna ganin hukumar hana fasakwauri ta yi gaggawar ‘daukar matakin.

Zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya na kan bakanta na ci gaba da hana shigowa da motocin don hakan ya raya tashar teku ta Apapa Legas, don samun bunkasar ‘kara tara kudaden shiga ga Najeriya, maimakon barin ‘yan Najeriya su rika kai kudin kasar Benin.

Kafin ta tafi hutu Majalisar Wakilai ta kada kuri’ar bukatar dakatar da matakin har sai an kammala nazari a kai. ‘Dan Majalisa Muhammadu Gudaji Kazaure, yace idan har ana bin doka a Najeriya babu dalilin da Majalisar ‘Kasa za tayi hukunci wani da aka nada yace ba hukunci bane.

Karayar tattalin arziki a Najeriya ta sanya hukumomi bin tsauraran matakan kudaden shiga da hakan ya sa aka bullo da wannan matakin.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Shigowa Da Motoci: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Shugaban Kwastam - 2'59"