Shigar Turkiyya Cikin Kungiyar Kasashen Turai Ta EU Na Fuskantar Koma Baya

Burin kasar Turkiyya na zama mambar kungiyar kasashen Turai ya sake samun koma baya, bayan da kungiyar ta jefa ayar tambaya kan sahihancin tsarin demokaradiyyar da ya ke yadawa.

Kokarin Turkiyya na neman zama mamba a kungiyar kasashen Turai ta EU da alama yana fuskantar koma baya bayan da bangaren zartarwar kungiyar ya fada a jiya Talata cewa bai ji dadin abinda ya kira gazawar da Turkiyyar ta yi ba wajen raya dimokradiyya da yaki da rashawa.

A rahotonsa na shekara-shekara, kwamitin zartarwar na EU ya ce Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya mallaka ma kansa iko mai yawa a harkar siyasar kasar, abinda ya kawo tabarbarewar tattalin arziki da ‘yancin fannin shari’ar kasar. Rahoton ya kuma ce hukumomin Turkiyya na ci gaba da matsin lamba ga kungiyoyin al’umma da kuma kafafen yada labarai.

Har yanzu Turkiyya muhimmiyar kasar huldar tarayyar Turai ce. Ko da ya ke, Turkiyya na ci gaba da kara nisa da EU saboda koma bayan da take samu sosai a bangarorin dimokradiyya, dokokin kasa, hakkokin bil’adama da kuma yin katsalandan a fannin shari’a, a cewar kwamitin.

Amma Turkiyya, da ta fara tattaunawar neman zama mamba a kungiyar EU a shekarar 2005, ta yi watsi da caccakar da kwamitin yayi mata, ta na bayyana ta a matsayin nuna wariya, a cewar kamfanin dillancin labaran AP.