Shelkwatar tsaro ta Najeriya ta musanta zargin faruwar wasu al’amura da ba’a saba gani ba da ya sabbaba zargin yunkurin juyin mulki a kasar da wata kafar yada labarai ta intanet ta yada ta na mai cewa hakan ya yi sanadin "sanya dakarun tsaron adar Shugaban Kasa cikin shirin ko-ta-kwana.
Wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Brigadiya Janar Tukur Gusau, ya fitar ya ce "an ankarar da shelkwatar tsaron Najeriya game da wani labari mara tushe da aka wallafa a mujallar yanar gizo a ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki, wacce ke ikirarin cewar an sanya dakarun tsaron Fadar Shugaban Kasa cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon faruwar wasu al’amura da ba’a saba gani ba, abinda ya sabbaba zargin yunkurin juyin mulki a kasar".
Mujallar ta kuma kara da cewar, zargin ya sabbaba ganawar gaggawa tsakanin Shugaban Kasa Bola Tinubu da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa da kuma Babban Kwamandan Askarawan Tsaron Fadar ta Aso Rock.
Sai dai shelkwatar tsaron Najeriyar ta fito ta bayyana cewar “babu kamshin gaskiya game da wannan zargin.
“Domin kawar da shakku, babban aikin da doka ta dorawa rundunar tsaron shine bada kariya ga fadar shugaban kasa harma da birnin tarayya abuja da kewayensa.
“Don haka, ya kamata a san cewar koda yaushe rundunar na zama cikin shirin ko ta kwana domin sauke nauyin daya rataya a wuyanta” a cewar sanarwar.
A baya-bayannan, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya sha nanata aniyar rundunar sojin Najeriya na bada kariya tare da bunkasa tsarin dimokradiya a Najeriya.