Shelkwatar Tsaro ta Tabbatar Da Mutuwar Sojoji 6 A Harin Borno

Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba

An sakaya sunayen sojojin da suka mutu har sai an sanar da iyalansu.

Shelkwatar tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta tabbatar da mutuwar ’yan ta’adda 34 da sojoji shida a wani harin da aka kai sansanin soji da ke Sabon Gari, ƙaramar hukumar Damboa a Jihar Borno.

Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba

Ya ce an sakaya sunayen sojojin da suka mutu har sai an sanar da iyalansu.

'Yan Boko Haram da dama ne suka kai hari sansanonin soji dake Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, a jihar Borno, lamarin da yakai ga yan Boko Haram da sojoji fafatawa tare da kashe wasu sojoji da yan banga, inda rahotonni ke bayyana cewa sojojin sun yi nasaran kashe wasu yan Boko Haram.

Saurari rahoton Ibrahim Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

Shelkwatar Tsaro ta Tabbatar Da Mutuwar Sojoji 6 A Harin Born0