Shugaban kungiyar Boko Haram ta masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama a Najeriya ya ce 'yan mata 'yan makarantar boko dari biyu da goma sha tara (219) da aka sace a garin Chibok a watan Afrilu, dukan su sun karbi addinin Islama kuma an aurar da su baki daya.
Abubakar Shekau ya fada a cikin wani bidiyo cewa 'yan matan wadanda yanzu haka su na gidajen mazan su, sun haddace juzu'in Amma a Alqura'ani .
Tun a kwanakin baya gwamnatin Najeriya ta yi sanarwar cewa ta na cikin tattaunawa da Boko Haram don a saki 'yan matan. Amma Abubakar Shekau ya karyata wannan labari, kuma ya ce shi bai ma san wannan mutumin dake ta fitowa ya na ikirarin cewa shi ne wakilin Boko Haram a tattaunawar ba.
Your browser doesn’t support HTML5
Shekau ya ce maganar 'yan matan nan fa ta wuce tun ba yau ba.
A farkon makon nan kungiyar kare hakkokin bil Adama ta Human Rights Watch ta wallafa wani rahoton cewa Boko Haram na rike da mata da 'yan mata fiye da dari biyar (500) kuma auren dole ya zama ruwan dare a sansanonin kungiyar. Wata wadda Allah Ya kubutar ta shaidawa kungiyar Human Rights Watch cewa ta ga 'yan matan Chibok ana sa su suna yiwa sauran mata aikace-aikace irin su girki da shara da wanke-wanke.
Kungiyar Human Rights Watch ta ce wadannan bayanai sun nuna cewa gwamnatin kasar Najeriya ta kasa kare lafiyar mata da ta 'yan mata daga dimbin abubuwan gallazawa da azabtarwa, kuma ta ce Najeriya ta kasa bincike, da gurfanar da masu aikata hakan a gaban shari'a.
Har wa yau kuma a cikin bidiyon, da yake magana a kan wani batu na daban shugaban Boko Haram Shekau ya ce su na rike da wani dan kasar Jamus da suka kama.