Shekaru Hudu Na Mulkin Mahamadou Issoufou

Mahamadou Issoufou

Shin wane ci gaba aka samu bayan shekaru hudu na mulkin shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou? Abokin aikinmu Adili Toro ya hada mana rahoton musamman don yin tsokaci ga cikar shekaru hudun shugaban da ya cika a shekaran jiya 7 ga Afrilun 2015.

Shugaban kasar jamhuriyar Niger Mahamadou Issoufou ya cika shekaru hudu a karagar mulkin kasar. Wasu daga cikin magoya bayan shugaban suna ganin an sami gagarumin ci gaba a kasar. Wani ma’aikacin gwamnati mai suna Muhammadu Adili yace, “daga shekaru 4 baya zuwa yanzu an sami gagarumin ci gaba a Nijar. Musamman maganar ruwan sha da amfanin yau da kullum don talakawa”.

Ya kara da cewa hatta kiwon lafiya ya in ganta don in kaje asibitoci zaka ga yadda magunguna da kulawa suka karu sannan an gina gidajen likitocin. Su kuwa ‘yan adawa bah aka yake a wajensu ba domin kuwa Alhaji Doudou Rahama daraktan jam’iyya CDS Rahama gani yake ana kasa ne ana cewa ana ci gaba.

“Ni a wajena an sami kwarya-kwaryar ci gaba amma na mai hakar rijiya ne. Suna maganar sun gina makarantu amma ai ba shine kadai matsala ba duk da yake idan ba ilimin akwai matsala”. Inji Doudou Ya nuna cewa akwai matsalar rashin sanin ina ma adawar take tsakanin jam’iyyun.

Malam Mustapha Kadi yace an yi mulki cikin bata tsarin dimukuradiyya. Yana kirane ga shugaban su yi waiwauye kan tsarin siyasar kasar. Issoufou Arzika farar hula ne shima a birnin Yemai inda ya nuna cewa yawancin ma’aikatan gwamnatin Nijar sun fi damuwa da kansu fiye da aikin da aka wakilta su su yi.

Shugaban dai na Nijar yana gab da kamala wa’adinsa na farko na shekaru biyar. Sannan a tsarin dokar Nijar shugaban kasa na iya yin shugabanci na wa’adi biyu masu shekaru biyar-biyar wanda in ka hada shekaru goma Kenan.

Your browser doesn’t support HTML5

Shekaru Hudu Na Mulkin Mahamadou Issoufou - 4'24"