Tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan wata kungiya mai suna Bring Back Our Girls, BBOG ta kunno kai tana fafutikan ganin an sakosu.
Kungiyar ta kama fegi a Fountain Square cikin birnin Abuja inda kullum take fitowa tana jawabi akan ya zama wajibi gwamnati ta kwato 'yan matan. Duk da matsawar da gwamnatin da ta shude tayi masu, 'yan kungiyar basu daina bayyana kansu ba. Gwamnati ta yanzu ta barsu suna cigaba da fafutikansu har ma ta shirya masu ziyara zuwa dajin Sambisa domin gani da ido irin kokarin da sojoji keyi.
Muryar Amurka ta tuntubi daya daga cikin shugabannin kungiyar BBOG Dr. Emma Shehu akan inda ake yanzu dangane da sauran 'yan mata 195 da har yanzu suna hannun kungiyar Boko Haram duk da ikirarin gwamnati na cewa ta tarwatsa 'yan ta'addan daga inda suka ja daga a dajin Sambisa.
Dr Emma Shehu yace har yanzu suna fafutika da gwamnati Najeriya domin ita ce take da hakkin kwato 'yan mata 195 da suke hannun 'yan ta'addan. Yace dole ne su cigaba da fafutikarsu. Yace kowanene shugaban kasa dole ne ya kwato 'yan matan bisa ga kundun tsarin mulkin kasa.
Akan ko wane kokari gwamnati ta keyi dangane da kwatosu, Dr Shehu yace basu da masaniya domin gwamnati bata bada bayani akan lamarin. Yace abun da yakamata gwamnati tayi shi ne tayi bayanai bayan an karbo 'yan mata 21 bara ba wai ta dinga kallon mutane ba kamar basu san abun da su keyi ba.
Dr. Shehu yace a mulkin dimokradiya dole ana yi ana yiwa mutane bayani. Injishi idan tattaunawar da gwamnati keyi ta tabarbare ta fito ta bayyanawa jama'a. Yace tun watan goma na shekarar da ta shude, har yanzu babu wani bayani da gwamnati ta sake bayarwa.
A cewar Dr Shehu ta samu 'yan mata 21 bisa ga umurnin da BBOG ta bayar na cewa karfin soji ba zai kaiga nasara ba sai da tattaunawa, kuma abun da gwamnatin tayi ke na.
Rashin bada bayani yana cikin matsalalolin da gwamnatin Buhar ke fuskanta.
Yau kungiyar BBOG ta kammala bikin tunawa da 'yan matan Chibok din tare da shirya lekca. Mai Martaba Sarkin Kano yana cikin wadanda suka yi jawabi yau.
Inji Dr Shehu SarkinKano Muhammad Sanusi II ya sake jaddada illar da cigaba da rike 'yan matan zai yiwa ilimin mata a rewacin Najeriya. Yace sace 'yan matan ya karyawa iyaye gwuiwa. Suna dari dari da barin 'ya'ya mata zuwa makaranta saboda suna misali da abun da ya faru da 'yan matan Chibok. Sarkin yace ba za'a samu 'yancin 'yan mata ba sai an kula dasu a makarantu su samu ilimi cikin tsanaki.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5