Shekara Daya Da Rabi Ba A Samu Bullar Polio A Jigawa Ba

Kwamishinan kiwon lafiya, Dr. Abubakar Tafida, yace gwamnati zata ci gaba da kokarin tabbatar da cewa ba a samu bullar shan inna a jihar ba.
Kwamishinan kiwon lafiya na Jihar Jigawa yace yau shekara daya da rabi ke nan rabon da a samu wani wanda ya kamu da cutar shan inna ta Polio a Jihar.

Dr. Abubakar Tafida ya bayyana wannan a lokacin kaddamar da sabon zagayen aikin rigakafin Polio na watan Maris a garin Madobi dake yankin karamar hukumarf Dutse ta Jihar.

Yace dukufa ga aikin rigakafin da aka saba yi wata wata a jihar ya taimaka gaya wajen jan burki ma wannan cuta, kuma gwamnati zata ci gaba da himmar tabbatar da cewa ba a sake samun bullar shan inna a jihar ba.

Shugaban kwamitin yaki da Polio na Jihar Jigawam kuma mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Mahmud Gumel, yace an samu nasarar yaki da Polio ne a saboda hadin kan da aka samu na iyaye, sarakuna, malaman addini da kuma ma’aikatan kiwon lafiya na jihar.

Yace tilas a ci gaba da kokari sosai wajen yin rigakafin a saboda barazanar da Jigawa take fuskanta daga jihohi makwabta inda har yanzu akwai wannan cuta ta shan inna ko Polio.