Wani malamin addinin Musulunci ya yi bayanin cewa Arafat shi ne rukuni mafi girma daga cikin rukunnan aikin Haji. Da ya ke amsa tambayoyi daga Ibrahim Alfa Ahmed na Muryar Amurka game da Ranar Arfa da Hawan Arfa, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri ya ce “Annabi Muhammad (SAW) ya ce: al-Hajju Arafat; wato tsayuwar Arfa ne ma kusan aikin Hajin gaba daya.
Ya ce Alhazai sun hallara daga sassa dabandaban na duniya, maza da mata. Ya ce an fara tsayuwar Arfa din ne bayan sallar Azahar da La’asar a matsayin Kasaru (Raka’o’I biyu) sannan daga nan tsayuwar ta fara. Ya ce dukkan Alhazai na ta addu’o’I – yawancinsu a tsaye amma akwai wasu a zaune wasu kuma a kwance kamar dai yadda
Musulunci ya yadda a yi.
Sheihk Duguri ya ce ana ta karatun Alkur’ani da Hailala da kuma neman alherin duniya da lahira wa kai da iyali da ‘yan’uwa da kasa da kuma duniyar Musulmi baki daya. Ya ce ranar Arfa na da Muhimmaci- ba ga Alhazai kawai ba, amma har da sauran Musulmin duniya wadanda su kuma su ke wani azumi mai muhimmanci na sunna.