Sabon babin da kasar Mali ta bude na shimfida hanyar maida mulki daga hannun sojoji zuwa hannun farar hula, tsari ne da zai iya dasa turakun zaman lafiya da daidato a yankin Sahel da ke yammacin Afirka a cewar jakadan Amurka na musamman da ke kula da yankin J. Peter Pham.
WASHINGTON D.C. —
A ‘yan kwanakin nan Pham ya zaiyarci yankin na Sahel, inda ya kara da cewa, duk da cewa hanyar da kasar ta dauka ta komawa mulkin farar hula – abin a yaba ne, amma yana ganin har yanzu akwai sauran jan aiki a gaba.
Shin wadanne matakai Amurkan take ba Mali shawara ta kiyaye domin kaucewa komawa gidan jiya, yau batun da za mu mayar da hankali akai kenan a cikin shirin na Duniyar Amurka. A yi sauraro lafiya.
Your browser doesn’t support HTML5