Dadadden jarumi, kuma mai shirya fina-finai nha kasar Indiya, Shashi Kapoor, ya rasu yau litinin yana da shekaru 79 da haihuwa.
Shashi Kapoor, wanda ya fito a matsayin jarumi a fina-finai fiye da 150, ya rasu a wani asibiti a birnin Mumbai, bayan da yayi fama da ciwon koda na shekara da shekaru.
Wani dan'uwansa mai suna Randhir Kapoor, wanda shi ma jarumi ne mai fitowa a fina-finan Indiya, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Press Trust of India cewa a gobe talata za a yi jana'izarsa.
Shashi Kapoor ya mutu ya bar 'ya;ya uku. Matarsa, jennifer Kendall, wadda ita ma jaruma ce a Britaniya, ta rasu tun shekarar 1984.
Sau uku Kapoor yana lashe zakaran jaruman fim na Indiya na kasa. Watakila fim dinsa da mutane da yawa zasu fi tunawa da shi shine "Deewar" wadda aka yi a shekarar 1975, inda ya fito tare da Amitabh Bachchan, inda kuma ya fadi wasu kalmomin da kusan duk mai sha'awar fim din Indiya ya rike su da ka, watau "Mere Paas Maa hai" (Ma'ana, Mahaifiya tana tare da ni, ko tana bangare na).
Shashi Kapoor na daya daga cikin jaruman fim na Indiya da suka fara fita cikin wasu bfina-finai na kasashen waje.
Firayim ministan Indiya, Narendra Modi, ya aike da sakon ta'aziyyarsa dazu ta hanyar Twitter, inda yace "za a jima ana tunawa da irin hazaka da muhibbar Shashi Kapoor a fagen fina-finan Indiya."