Sharudan Aikin Hajji Na Wannan Shekarar

Hoton Masallacin Ka'aba

Gwamnatin Saudi Arabia ta fitar da sharuda 6 gabanin aikin hajjin wannan shekarar.

A cewar ministan harkokin lafiyan kasar, Tawfiq Al-Rabiah wadanda ba su kai shekara 65 ne ba kawai za su Iya gudanar da aikin na Hajj.

Wadanda ke fama da wasu cututtuka masu tsanani ma ba za su Iya gudanar da aikin ba.

Hakan na zuwa kwana 1 bayan da hukukomi a kasar su ka bayyana cewa 'yan kasashen wane ba za su iya zuwa aikin hajjin bana ba, sai wadanda ke zaune a cikin Saudiyyar.

Yadda aka gudanar da aikin Hajji a shekarar 2019

Duk wadanda zasu zo hajjin kuma, sai an gudanar da gwajin cutar Coronavirus a kansa kafin a basu damar shiga masalatan.

Ministan ya kara da cewa, dole sai mahajjatan sun bar tazara a tsakaninsu, kuma ana ganin cewa ba za a wuce baiwa mahajjata 10,000 damar gudanar da aikin hajjin ba.

Bayan gama aikin, za a tilasta wa mutane su kebe kansu na kwanaki 14.

A kowace shekara dai a kalla Mutum miliyan 2 a duk fadin duniya ne ke gudanar da aikin hajjin a kasar ta Saudiyya.