Sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra’ayin Gwamnatin Amurka
Tun daga farko, shugaba Joe Biden ya bayyana karara cewa ya dauki yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kasa da na cikin gida, a matsayin wani babban abin da ya shafi tsaron kasa da kuma abin bai wa fifiko a manufofin kasashen wajen Amurka.
Dalili kuwa shi ne cin hanci da rashawa ya na kawo rashin yadda, yana kashe gwiwa game da cibiyoyin dimokaradiyya, da hana ci gaban tattalin arziki. Daga karshe dai ’yan kasa ne su ke fama da wannan sakamakon yayin da farashi ke ta tashi, ake kuma kashe kudi kalilan kawai kan abubuwan da su ka shafi jama’a, kuma muhalli na lalacewa.
Don haka ne fadar White House ta fitar da dabarun yaki da cin hanci da rashawa na Amurka na farko, wadanda za su samar da tsarin yadda Amurka za ta dau mataki kan cin hanci da rashawa da kuma laifukan da ke da alaka da su. Don haɗa kai da haɓaka yaƙi da cin hanci da rashawa a duk fannoni na diflomasiyyar Amurka da taimakon ƙasashen waje, Shugaba Biden ya nada Richard Nephew a matsayin mai kula da ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a duniya na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Da yake magana a wani taron manema labarai a karshen watan da ya gabata [25 ga Agusta, 2022], mai kula da tsarin aikin Nephew ya ce "Tsarin "an tsara shi ne cikin ginshiƙai biyar masu ƙarfafa juna."
Na farko shi ne na zamanantarwa, tsarawa, da samo hanyoyin gwamnatin Amurka na dakile cin hanci da rashawa. Na biyu shine dakile haramtattun harkokin kudi. Na uku, kama masu cin hanci da rashawa. Na hudu, kiyayewa da karfafa shirin yaki da cin hanci da rashawa ta fannoni da yawa. Na biyar, inganta huldar diflomasiyya da amfani da albarkatun taimakon kasashen waje don cimma manufofin yaki da cin hanci da rashawa."
Aiwatar da da dabarun yaki da cin hanci da rashawa na kunshe da abubuwa da dama da ke bukatar kulawa ta musamman.
Na farko," mai kula da tsarin, Nephew ya ce, "mu na aiki don kintsa dukkan hanyoyin yaƙi da cin hanci da rashawa."
"Cigaba na hakika na bukatar sauye-sauye da ci gaba da sa himma daga dukkan bangarorin ke yi don cimma sakamako, wanda aka sanar da su ta hanyar fahimtar abin da ke aiki a cikin yanayi na musamman da kuma wasu kasashe."
Na biyu, muna aiki don inganta ayyukan al'umma mai yaki da cin hanci da rashawa da kuma karfafa aiwatar da kudurorin yaki da cin hanci da rashawa."
“Na uku, Amurka za ta ci gaba da taka rawar jagoranci wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma za mu yi hakan tare da hadin gwiwar kasashe da kungiyoyi da dama da suka sadaukar da kansu ga wannan harka. .”
A ƙarshe, Amurka "za ta dubi yadda za ta ƙarfafa ƙa'idodinmu na cikin gida da dokokinmu, [don ganin] abin da za mu iya yi don tabbatar da cewa lallai tsare tsarenmu mafiya kyau sun yi cikakkiyar inganta," a cewar Nephew. "Babu wata hanya mai sauki ta magance cin hanci da rashawa," in ji shi. "Dukkanmu muna cikin wannan gwagwarmaya tare, kuma dukkanmu muna fuskantar wannan kalubalen da muke fama da shi." Sanarwa: Wannan shi ne sharhin Muryar
Amurka; mai bayyana ra’ayin Gwamnatin Amurka.