"Sai dai abin takaici, kungiyoyin mayaka masu alaka da Iran na barazanar lalata nasarorin da kasar Iraki ta samu tun bayan fatattakar 'yan ISIS/Da'esh a yankin shekaru bakwai da suka gabata."
"Tun daga watan Oktoban 2023, waɗannan ƙungiyoyin sun kai hari kan sojojin Amurka da na haɗin gwiwa a Iraki, Siriya, da Jordan fiye da lokuta 165."
"Abin takaici, an kashe sojojin Amurka uku tare da jikkata wasu da dama a ranar 28 ga watan Janairu a lokacin da kungiyoyin mayaka masu alaka da Iran suka kai hari kan sojojin Amurka da ke Jordan domin su taka rawa a yaki da 'yan ISIS."
“Wannan asarar mai zafi ce. Ba abun da za mu yarda da shi ba ne. Kuma ba zai yiwu a ci gaba da kai irin wadannan hare-haren ba."
Ofishin ba da tallafi na Majalisar Dinkin Duniya na Iraki, ko UNAMI, har yanzu na da sauran muhimmin aiki a gaba.
Amurka na karfafa ofishin UNAMI don ta taimaka wa hukumar zaben Iraki mai zaman kanta don shirya zaben 'yan majalisar dokokin yankin Kurdawa da na Iraki a karshen wannan bazarar ba tare da bata lokaci ba.
"Muna kuma karfafa gwiwar ofishin UNAMI akan taimakawa gwamnatin Iraki a kokarinta na kare hakkin bil'adama da kuma yaki da rashin hukunta masu aikata laifuka."
A matsayinta na kasar kawancemu a yankin, Amurka na fatan ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Iraki wajen samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.