Kungiyoyin kwallon kafa 4 masu buga gasar Firimiya Lig na kasar Ingila, sun kai wasan karshe a gasar Turai ta UEFA Champions league, da kuma Europa Cup na bana, kungiyoyin sun hada da Tottenham, Liverpool, Chelsea da Arsenal.
Arsenal zata buga wasan karshe da Chelsea bangaren Europa Cup, bayan da ta samu nasarar doke takwararta Valencia da ci 7-3 a jimlar wasanni biyu da suka fafata a matakin wasan daf da na karshe. A karawar su ta farko Arsenal ta sha da ci 3-1 sai haduwar su ta biyu ta sake cin 4-2, hakan ya bata damar fitowa wasan karshe.
Ita kuwa Chelsea a karawar su ta farko da Eintracht Frankfurt a Jamus, an tashi da 1-1 sai kuma karawa ta biyu a ranar Alhamis da ta gabata a Ingila, nan ma aka shafe mintoci 120 inda ta sami 1-1. Daga bisani akayi bugun daga kai sai mai tsaron gida wato Penalty, inda Chelsea ta sami nasara da ci 4-3 wanda ya bata damar tsallakawa zu wasan karshe.
Bisa tarihi wannan ne karon farko da kungiyoyi hudu daga kasa daya za su buga wasan karshe na gasar Champions League da na Europa Cup a kaka guda.
A bangaren gasar zakarun Turai na Uefa Champions league kuma, Tottenham zata kara da Liverpool bayan da ta yi waje da Ajax a matakin wasan daf da karshe.
Bangaren Europa Cup Chelsea za ta fafata da Arsenal a wasan karshe,
a Baku, babban Birnin Azerbaijan ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekarar ta 2019. Ita kuma Tottenham da Liverpool zasu fafata a wasan karshe na gasar Champions League ranar 1 ga watan Yuni a Birnin Madrid na kasar Spain.