Shahararren Mawakin Hausa Hassan Wayam Ya Rasu

Kalangu

Shararren Mawaken Hausa nan, Alhaji Hassan Wayam ya rasu yana dan shekaru 76 a gidansa da ke Zaria, Jihar Kaduna.

Shahararren mawakin Hausa nan, Alhaji Hassan Wayam, ya rasu a daren Asabar da misalin karfe 3:30 na tsakar dare.

Wani rahoto da Jaridar Leadership ta wallafa ya ce, Dan ga Marigayin, Bello Hassan Wayam, shi ne ya tabbatar da rasuwar tasa a wata zantawa da shi ta wayar tarho.

Marigayi Hassan Wayam a rasu ya na da shekaru 76, inda ya bar mata daya da ‘ya’ya 11 da kuma jikoki da dama.


Ya rasu ne a gidansa da ke Zaria a Jihar Kaduna bayan wata jinya da ya yi fama da ita.

Tuni akayi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gidansa da ke Zaria, inda a ka binne shi a makabartar da ke garin.

Kafin rasuwarsa, Hassan Wayam wanda yasha fama da rashin lafiya mai tsanani, ya yi matukar tashe akan wakoyi da dama masu cike da hikima da kuma wa’azantarwa kamarsu “Ba ni ne na Fada ba”.

A lokuta da dama an sha wallafawa a Youtube da wasu shafukan sada zumunta ta yanar gizo cewa Hassan Wayam yana cikin wani hali dake bukatar taimako.