Shah Rukh Khan Da Salman Khan Zasu Sake Haduwa

Salman Khan

Ma’abota Shirin Bigg Boss, na Bollywood, lokaci yayi da zasu sake katari samu jarumai biyu Shah Rukh Khan da Salman Khan, a zauren shahararren shirin nan na Bollywood watau Bigg Boss. Jaruman dai sun kafa tarihi, a shirin Bigg Boss, a can baya.

Amma kuma idan har fitattun jaruman kasar Indiya, kamar su Shah Rukh Khan da Saman Khan, suka hadu a kowane lokaci toh, tabbaci hakika babu abinda zai biyo baya zai abin alajabi dana ban mamaki.

Hada wadanna jarumai, a wannan shirin na Bigg Boss, tabbas zai kawo annashuwa da Shewa ga masu kallo sa’ilinna hata masu shirya shirin suma zasu kasance cikin farin ciki domin hakarsu ta cimma ruwa na faratawa masu kallo rai.

Da alamun cewa lokaci yayi da masu shirya shirin na Bigg Boss, da mutanen gari zasu sake yin murna domin Shah Rukh Khan, a shirye yake da ya sake lekawa zauren Bigg Boss karo na goma shirin daya sami karbuwa a Indiya kuma mai yawan rikice rikice.

Jama’a dai a Bollywood dama kasar ta Indiya, farin cikin suke yi kasancewa jaruman biyu zasu sake haduwa a shirin na Bigg Boss.

Your browser doesn’t support HTML5

Shah Rukh Khan Da Salman Khan Zasu Sake Haduwa - 5'00"