Biyo bayan doke kungiyoyin wasa kwallon kafa na kasashen Zambia da Algeria, da kungiyar Super Eagles, ta Najeriya, tayi a ci gaba da wasani neman gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.
Mai horar da ‘yan wasan Gernot Rohr, ya nanata abinda ya fadi a lokacin da kungiyar ta Super Eagles, da lashe wasan da tayi tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta kasar Zambia, cewa shagalin murna ba yanzu ba, domin akwai sauran aiki a gaba.
Ya sake nanata maganar ne a lokacin da yake jawabi ka manema labarai bayan wasan da ‘yan Super Eagles suka buga da kasar Algeria, inda suka lallasa Algeria, da ci 3 da 1, a filin wasa na Godswill Akpabio, dake Uyo, a jihar Akwa Ibom.
Najeriya, na kan gaba a rukunin “B” inda kasar Kamaru ke biye mata kamar yadda Kamfanin dilancin labarai na Najeriya, ya ruwaito.
Mai horar da ‘yan wasan na Super Eagles, Gernot Rohr, ya kara da cewa akwai wasan sada zumunta da Najeriya, zata yi da kasar Masar, a watan Janairu, a Dubai, wanda zai bashi damar ganin wasan ‘yan wasan kungiyar na Super Eagles, na gida, koda yake yace zai ci gaba da sa ido akan ‘yan wasan da suke kasashen waje.
Your browser doesn’t support HTML5