Wani matashi ‘dan asalin Mexico mai suna Jose Espinoza, mai launin farar fata kamar ta turawa ya shafawa kansa bakin fenti domin gujewa kamun ‘yan sanda akan laifin da ake tuhumarsa dayi.
Jami’an tsaro na neman matashin mai shekaru 23 kan laifin satar mota a garin Fresno dake jihar California, da kuma laifin rashin bin umarnin alkali na jeka gyara halinka.
‘Yan sanda sun kama matashin har sau biyu yana kubucewa, domin kaucewa kamu na uku Jose yaje ya shafawa kansa bakin fenti, amma duk da haka ‘yan sandan sun cafke shi.
Hotan sa da ‘yan sandan keda shi ne ya tabbatar da shine mutumin da suke nema, a yanzu haka yana ‘daure a ofishin ‘yan sanda. ‘Yan sandan sunce sake kamanni bai yiwa matashin aiki ba.