'Yan Najeriya masu safarar miyagun kwayoyi akan kamasu a yanke masu hukuncin kisa a wasu kasashen duniya.
Kasashe irin su Sin, Malaysia, Singapore da Saudiya sun sha yiwa 'yan Najeriya hukuncin kisa sau tari kuma wasu a yi masu daurin rai da rai.
Yara matasa sukan mayarda wasu abubuwa kayan maye kamar shekan fetur, solisho, kashin kadangare, yayinda wasu mata kuma ke shan benelin na maganin mura don samun marisa koko dogon barci.
Malama Halima Baba Ahmed mai kemfen din kangarewar matasa ta yi karin bayani kan illar miyagun kwayoyi. Masu shan kwalba goma na maganin da ya kamata ya sha cikin kwanaki biyar ya jima kwakwalwarsa. Wanda kuma ya sha maganin da anfaninshi ya kare tamkar ya kashe kansa da kansa ke nan. Yana iya haukacewa gaba daya.
Shan magani ba tare da izinin likita ba nada nashi illar. Usman Funtuwa, jami'in kiwon lafiya yace maganin da ka ba kanka tana yiwuwa jikinka baya son maganin. Idan ka sha maimakon ya yi maka magani sai ya yi wata illar ta daban. Haka ma yiwa kai allura rigima ce da ka iya kaiga wani mugun lahani.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5