Seyi Makinde Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo

  • Hasan Tambuwal
    Murtala Sanyinna

Seyi Makinde

Hukumar Zaben Najeriya ta INEC ta bayyana Seyi Makinde a zaman wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Oyo na ranar Assabar.

Seyi Makande na jam'iyyar PDP ya sami lashe zaben gwamnan jihar Oyo, bayan nasarar samun mafi yawan kuri'u a zaben da aka gudanar a ranar Assabar, kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta bayyana.

Da ya ke bayyana sakamakon zaben gwamnan na jihar Oyo a ranar Lahadi, babban jami'in tattara sakamakon zabe na INEC a jihar, Adebayo Bamire, ya ce Makinde ya sami nasara a kananan hukumomi 31 na jihar, da suka ba shi adadin kuri'u 563,756.

Makinde ya doke manyan abokan takararsa na jam'iyyar APC Teslim Folarin wanda ya sami nasara a kananan hukumomi biyu da jumlar kuri'u 256,685, da kuma Adebayo Adelabu na jam'iyyar Accord Party, wanda ya zo na 3 da yawan kuri'u 38,357.