Sergio Ramos Yana Iya Nemar Wata Kungiya

Sergio Ramos

Dan wasan nan mai suna Toni Kroos na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, dake kasar Spain ya amince da ya ci gaba da zama a kungiyar ta Real Madrid, domin ci gaba da murza tamola har na tsawon shekaru shida masu zuwa inda zai kammala a shekara ta 2022.
Har ila yau shugaban kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez, ya ce tana iya yuwa kungiyar zata baiwa kaftin din kungiyar Sergio Ramos, damar da ya neme wata kungiya a karshen kakar wasan kwallon kafa na bana.
Ramos wanda ya taho Kungiyar ta Real tun shekara 2005, daga Sevilla, ya kwashe shekaru goma sha daya yana murzawa Real Madrid, tamola inda ya buga mata wasanni kusan dari biyar, koda yake a halin Sergio, ya tafi jinya na tsawon makonni 4.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na neman mai tsaron baya na Manchester United mai suna Matteo Darmian, Chelsea kuma na zawarcin dan wasan Atletico Madrid mai suna Carrasco.