Senata Aisha Jummai Alhassan ta zama mace farko data zama gwamna

Election official count gubernatorial ballot papers at the end of voting in one of the polling station in Lagos, Nigeria, April 11, 2015.

Senata Aisha Jummai Alhassan ta zama mace farko da aka zaba mukamin gwamnan a Nigeria bisa tafarkin mulkin Democradiya

A Nigeria Senata Aisha Jummai Alhassan ita kam ta shiga tarihi a zaman macen farko da aka zaba gwamna bisa tafarkin mulki democradiya, bayan da wata kotun daukaka kara a Abuja baban birnin taraiyar Nigeria ta ayyana ta a matsayin gwamnar jihar Taraba.

Senata Aisha Jummai Alhassan ta godewa Allah da dukkan magoya bayanta da suka taimaka da adu'a da wasu abubuwa a hira da wakiliyar sashen Hausa Medina Dauda ta yi da ita

Your browser doesn’t support HTML5

Senata Aisha Jummai Alhassan akan nasarar data samu 1.59

Haka suma shugabanin kungiyoyin mata da suka halara a gidan Senata Aisha bayan da kotun daukaka kara ta yanke hukunci, suna taya ta murna, sun baiyana jin dadin su kamar haka

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayin wasu mata akan nasarar da Senata Jummai Alhassan ta samu 2.41