Asusun da aka kaddamar a birnin Legas cibiyar kasuwanci a Najeriya zai zama tamkar asusu ne da zai tallafawa masu saka jari wajen rage hasara idan kamfanin da suke da hannun jari ya durkushe ko kuma hannun jarin ya salwanta.
Malam Munir Gwarzo babban darakta a hukumar SEC, wato hukumar dake kula da hada-hadar saka jari a Najeriya ya yi karin haske.
Yace kafa asusun zai sa hankalin masu saka hannun jari ya dawo saboda idan mutun ya saka kudi bai dawo ba amma kuma ba laifinsa ba ne asusun zai taimaka rage hasarar. To saidai ko nawa mutum ya saka a matsayin jari asusun ba zai ba mutum fiye da nera dubu dari biyu ba.
Yace sun dauki matakan hana kamfanonin rashin samun riba. Ba zasu bada cin hanci kafin su yi muamala ba a matsayin kai'dodi da zasu sa su cigaba. Wannan zai karfafa mutane dake da kudi a waje su dawo dasu su saka jari a kasar.
Su ma kamfaononin dake hada hada a Najeriya sun ce matakan zasu taimaka wurin habbaka tattalin arziki.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5