Bayan sauya wasu manyan jami’an soji da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sanadiyyar cigaba da kai hari da kungiyar Boko Haram ke yi, kwararru sun cigaba da bayyana ra’ayoyinsu. Galibi na cewa yadda aka yi shi ya fi kuma ba su yi mamaki ba ganin yadda har yanzu Boko Haram ke cigaba da barna.
Dr Sa’id Ahmed Dukawa na Sashin Kimiyyar Siyasa na Majami’ar Bayero ta Kano ya gaya wa abokin aikinmu Sahabo Imam Aliyu cewa ganin irin shakkar iyawa da kuma niyyar jami’an sojin da aka sauya, ga dukkan alamu matakin sauya jami’an sojin shi ya fi. Y ace kuma Buhari ya kauce ma garaje saboda ya dau lokaci na nazari kafin ya dau wannan matakin.
Da sahabo ya tambaye shi ko bai ganin canja sojojin a yanzu bayan ana yaki sosai da Boko Haram zai kawo nakasu gay akin sai y ace ganin yadda aka yi ta baiwa sojojin zarafi a bay aba tare da samun biyan bukata ba, akwai hikima a canja su ko a ga wani sabon abu.
Your browser doesn’t support HTML5