Masu iya magana na cewa rikicin duniya da mai rai ake yinsa. Wata yarinya mai suna Zainabu, tace saurayinta da suka dade suna soyayya ya yaudareta. Inda yace mahaifinsa ya hana shi aurenta ya kuma bata shawarar cewa suyi ciki domin baban nasa ya kyale su suyi aure.
Zainab ta fadi cewa sun fi shekara 3 da saurayin suna soyayya, amma da saurayin fada wa mahaifinsa cewa yana so yayi aure sai Baban yace bai amince ba. Zainab ta ba saurayin nata mai suna Buhari shawara cewa tunda mahaifinsa bai yi na'am da batun auren ba to ya hakura, ita kuma zata auri wani dan'uwanta da ya fito nemanta da aure.
Zainab ta cigaba da cewa, saurayin ya ki amincewa da shawarar da ta bashi har ma ya kira dan'uwan nata mai neman ta ya zazzage shi bayan haka kuma ya a yi wa yayanta rashin mutunci akan cewa da shi ake kulla munafuncin.
Saurayin dai ya yaudareta akan cewa idan ta yarda yayi mata ciki, mahaifinsa zai amince da aurensu.
Mahaifiyar Zainab ta shaidawa Baraka Bashir cewa, mahaifin saurayin ya nuna ya fi su karfi, su kuma basu da wani gata. hukumar Hisbah ce gatansu, don sune uwarsu da ubansu kuma tana fata za a taimaka mata akan irin rayuwar da aka jefa diyarta.
Rundunar hukumar Hisbah ta jihar Kano, ACG Nasiru Isah, yace sun gayyaci iyayen matasan biyu kuma da zarar sun gama bincike zasu tura su inda ya dace.