Saura 'Yan Sa'o'i A Fara Zakulo Mahaka Daga Karkashin Kasa A Chile

Ma'aikatan ceto wadanda za su yi kokarin zakulo mahakan su 33 daga karkashin kasa a Chile

An shirya za a fara gudanar da aikin ceto mutanen da karfe 12 na daren yau talata agogon kasar, misalin karfe 4 na asubahin laraba agogon Najeriya da Nijar.

A yankin arewacin kasar Chile, ‘yan sa’o’i kadan suka rage kafin masu aikin ceto su fara kokarin zakulo mahaka ma’adinai su 33 daga karkashin kasa zuwa kan doron kasa.

A jiya litinin, an samu nasarar yin gwajin gugar da za a yi amfani da ita wajen ceto mahakan. Wannan guga rufaffiya, wadda aka sanya mata suna Phoenix, fadinta ya kai rabin mita daya, tana kuma dauke da iskar shaka ta Oxygen da wayar tarhon da za a iya magana da masu aikin ceto da ita.

An shirya za a fara gudanar da aikin ceto mutanen da karfe 12 na daren yau talata agogon kasar, misalin karfe 4 na asubahin laraba agogon Najeriya da Nijar. Ana sa ran za a dauki kwanaki biyu wajen fito da mahakan daya bayan daya daga wannan ramin hakar ma’adinai.

Wadannan mahaka 32 ‘yan kasar Chile da guda daya dan kasar Bolivia sun kasance a karkashin kasa tun ranar 5 ga watan Agusta a lokacin da bakin ramin hakar ma’adinai mai suna San Jose ya rusa ya rutsa da su. Ministan kiwon lafiya na Chile, Jaime Manalich, ya ce alamu na baya-bayan nan sun nuna cewa mahakan su na cikin koshin lafiya duk da watanni biyu da kwanakin da suka shafe a karkashin kasa.