Yerima Salman Yayi Alwashin Maida Saudiyya Bisa Musulunci Mai Sassaucin Ra'ayi

Yerima Mohammed bin Salman.

Yerima Salman yace kashi 70 cikin dari na 'yan kasar matasa ne kasa da shekaru 30.

Guguwar canji dake kadawa a kasar Saudiyya ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki yana kayata wasu 'yan kasar, wasu kuma suna zura ido, masu ra'ayin mazan jiya kuma ku sun fusata ko sun dimauta.

Yerima Mohammed Ben Salman, ya gayawa taron wasu masu zuba jari a karshen watan 10 cewa, yana kokari ne ya "maida Saudiyya bisa tafarkin Islaman da aka san kasar na sassauci" kamin zuwan juyin juya halin Iran a 1979.

Ya jaddada cewa kashi 70 cikin dari na mutan kasar matasa ner kasa da shekaru 30, daga nan yayi alwashin "ba zai bata shekaru 30 masu zuwa suna raye karkashin manufofi na tsatsatsauran ra'ayi ba."

Clarence Rodriguez, wacce shekaru 12 tana zaman wakiliyar wata kafar yada labaran Faransa a Riyadh, kuma a baya bayan nan ta rubuta littafi mai suna "Saudi Arabia 3.0" wadda ya maida hankali kan burin matan kasar Saudiyya da matsa, ta gayawa Muriyar Amurka cewa, ta hakikance cewa Saudiyya "tana cikin rudani" saboda faduwar farashin mai," saboda haka ta fada tsaka mia wuya wadda ya zama tilas ta "sauya fasalin tattalin arzikinta, wadda hakan ya tilasta yin wasu sauye sauye ta fuskar zamantakewa da suka shafi mata da kuma matasa."