Kasar Saudiyya ta kama wasu mutane 8, ciki har da Amurkawa biyu ‘yan asalin Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayyana cewa cikin mutanen da aka tsare har da wata mace mai juna biyu da maza 7.
Duka mutanen da aka kama sun sha nuna goyon bayan kan kare hakkokin mata da ke kasar.
Wata kungiyar kare hakkin bil Adama da ake klira, ALQST, wacce ke da hedkwata a London, ta ce duka mutanen da aka kama marubuta ne da kuma masu rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta, wadanda a baya suka bayyana ra’ayoyinsu a fili akan yin sauye-sauye.
“Ya ce batun tauye hakkin dan Adama, abu ne da ya zama ruwan dare a wannan yankin, amma kuma babu abin da ake yi, kuma an sha magana akai, kuma ban ga wata alama da ke nuna cewa hakan ya shafar huldar diplomasiyya ba." Inji Said Sadek, malami da ke koyarwa a fannin kimiyyar siyasa da halayyar dan adam a kasar Masar.
A ranar Alhamis aka kama yawancin mutanen.
Daga cikin wadanda aka kaman, har da Badr al-Ibrahim, wanda marubuci ne kuma likita kuma, wanda har ila yau Ba’amurke ne dan asalin kasar ta Saudiyya.