Inji rahoton da kafofin yada labarai na kasar Saudiyan Sarkin zai biya kwatankwacin nera miliyan sittin kan duk wanda ya rasu sanadiyar hatsarin da ya auku.
Kowane mutum kuma da ya jikata zai samu kwatankwacin nera miliyan talatin. Bayan wadannan duk wanda ya samu nakasa ta din-din din shi ma zai samu nera miliyan sittin.
Dangane da wadanda suka samu jikatar da ta hanasu saukar da farali a wannan karon Sarkin ya dauki nauyinsu da su dawo shekara mai zuwa su sauke faralin. Sarkin bai tsaya nan ba. Za'a ba iyalan wadanda suke asibiti takardar bizar shiga kasar domin su yi zaman jiyar 'yanuwansu.
Matakin da sarkin ya dauka ya farantawa kungiyoyin musulmai.
Shugaban IZALA a Najeriya Shaikh Abdullahi Bala Lau ya yabawa sarkin da daukan matakin da ya dauka na biyan diya da taimako. Yace abun yabawa ne Allah kuma ya saka wa sarkin saboda kulawa da haki da jinin al'ummar Musulmi. Abun da sarkin ya yi ya nuna kyakayawan shugabanci. Matakin ya kare daraja da martabar al'ummar musulmi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5