Saudiya Ta Soma Biyan Hakkin Wadanda Suka Rasa Rayukansu A Turaraniyar Bara

Ofishin Hukumar Alhazan Jihar Adamawa

Hukumomin Kasar Saudiya tare da hadin gwiwar hukumar mahajjata ta Najeriya sun mikawa magadan Alhazai goma sha biyu na jihar Adamawa da suka rasa ransu a turairainiyar da ta abku lokacin akin hajjin 2015 kaddarorinsu.

Babban sakataren hukumar kula da jin dadin mahajjata na jihar Adamawa Injiniya Umaru Bobboi ya shaidawa muryar Amurka cewa maido da kaddarorin wadanda suka rasun ya dauki tsawon lokaci ne saboda nazari mai zurfi da hukumomin suka yi wanjen tantance wadanda suka rasu da kuma magadansu.

Babban sakataren ya ce darasin da 'yan Najeriya musamman jami'an tsaro yakamata su yi koyi da shi shine na rikon amana da tsare gaskiya.

Cikin juyayi da tausayi daya daga cikin magadan Alhaji Lekki ya jinjinawa hukumomin Saudiya da na alhazan Najeriya da rikon amanar marayu.

Wakilin sashin Hausa Sanusi Adamu ya nemi jin yadda majalisar gamayyar kungiyoyin Musulmai ta bakin mataimakin shugaban kungiyar Malam Gambo Jika suke kallon wannan mataki na hukumomin Kasar saudiyya na maidawa marayu hakkokinsu, ya ce matakin na hukumomin Saudiyya suka dauka ya Kara kyakkawar gurbi dadai da koyarwar addinin Musulumci.

Bayaga mahajjata goma sha biyu da aka tantance gawarsu akwai mutane biyu da ba a ga gawarsu ba gamma aka bada tabbacin rasuwarsu bayan an dauki sanfarin jin in 'ya,yansu da name mahaifansu mata.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Saudiya Ta Soma Biyan Hakkin Wadanda Suka Rasa Rayukansu A Turaraniyar Bara - 3' 12"