Saudiya Ta Bukaci Kara Tantance Alhazan Najeriya Saboda Cutar Zazzabin Lassa

Alhazai a birnin Makka

Sanadiyar rahoton barkewar zazzabin lassa makon jiya ya sa mahukumtan Saudiya suka bukaci a yiwa alhazan Najeriya binciken kwakwaf domin a tabbatar babu wanda yake dauke da kwayar cutar da zai je aikin hajjin bana

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Najeriya ta ce ta yiwa cutar zazzabin lassa kwaf daya saboda a cewar ta yanzu mutum daya ne ke dauke kwayar cutar a duk fadin kasar.

Wannan ikirarin ya biyo bayan wata sanarwa da hukumar kiwon lafiya ta kasar Saudiya ta fitar inda take cewa a dauki matakan kara tantance duk alhazan Najeriya, daga su har jakukkunansu domin a tabbatar babu wanda yake dauke da cutar zazzabin lassa ko bera a jakarsa.

Ma’aikatar ta Saudiya ta dauki matakin ne biyo bayan labarin bullar cutar a jihar Adamawa makon jiya.

Shugaban hukumar alhazan Najeriya Abdullahi Mukhtar ya yi karin haske akan shawarwarin da aka cimma a taronsu. Injishi sun yi alkawarin cewa hukumomin alhazai na jihohi zasu tantance jakunan alhazansu da duk kayan da alhazan zasu dauka domin a tabbatar duk wani halitta dake dauke da cutar ba’a barshi ya je aikin hajji ba bana.

Shugaban ma’aikatan kiwon lafiya na hukumar alhazai Dr. Ibrahim Kana ya ce suna da wata kyakyawar dangantaka da hukumomin Saudiya saboda haka matakan da suka dauka zasu gamsar dasu. Baicin hakan akwai hukumar kiwon lafiya ta duniya dake tsakaninsu.

Cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban hukumar alhazai ta jihar Zamfara Abubakar Sarkin Pawa Zanko, wanda ya yi bayanin matakan wayar da kawunan alhazan. Yace duk matakan da jihohi zasu dauka a shirye suke su daukesu domin tabbatar cewa babu wata matsala da ta sake kunno kai.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Saudiya Ta Bukaci Kara Tantance Alhazan Najeriya Saboda Zazzabin Lassa - 3' 15"