Kasar Saudiyya ta kama fiyeda mutane 400, galibinsu 'yan kasar kan zarghin suna da alaka da kungiyar ISIS.
A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fitar da kamfanin dillancin labarai na kasar ta wallafa, tace kama mutanen wani banagare ne na gagarumin matakin tsaro da kasar ta dauka domin dakile wani shirin kai hare hare da kungiyar ISIS ta shiya zata kai kan masallatai, da wani ofishin jakadanci, da ofisoshin jami'an tsaro, dana gwamnati a lardin Sharurah na kasar.
Wannan sanarwa tana zuwa ne kwana daya bayan kungiyar ta ISIS ta kai hari kan waa kasuwa cike makil da jama'a a lardin Diyala a Iraqi ta kashe mutane 115.