Saudi Arabia Zata Bude Hanyar Shiga da Kayan Agaji a Yaman

Hukumomin Saudi Arabia

Saudi Arabia tace zata bude tashar jiragen ruwa da yan tawayen Houthi na Yeman ke rike da shi domin shigar da kayan agaji na jin kai har tsawon kwanaki 30 duk da harin makami mai lizzami da yan tawayen suka kai a yankin Saudia.

Saudia ta kuma ce zata kawo sababbin na’urorin jigilar kaya a tashar jiragen ruwa don su taimaka wurin sauke kayan a cikin jirgin ruwa.

Rundunar hadin gwiwa karkashin jagorancin Saudia tana kokarin kora yan tawayen Houthi daga Yemen da suka yiwa tashar jiragen sama da na ruwa a kasar zobe a wata da ta gabata bayan da ta kaiwa filin saukar jiragen sama na Riyadh harin makami mai lizzami.

A halin yanzu kuma, ministan harkokin wajen Iran Mohammad Jayad Zarif ya fadawa manema labarai a jiya Laraba cewar Iran zata bi diddigin wannan zargin karya da Amurka tayi cewar Tehran ce ke baiwa yan tawayen Houthi makamai.

Zarif ya kira yunkurin Amurka takala kuma yace Amurka tana kokarin boye goyon bayan da take bayarwa kashe Yamanawa da bau san hawa ba basu san sauka ba, shi yasa take wannan zargi.