Kimanin shekaru shida kenan da aka sace ‘yan matan a garin Chibok da ke arewa maso gabashin Najeriya a wani samame da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a makarantar sakandaren a shekarar 2014 kana suka yi awon gaba da ‘yan mata 220.
A cikin shekarar 2017 ne hukumomin Najeriya suka karbo wasu a cikin ‘yan mata a wata musayar da gwamnatin ita ma ta saki wasu ‘yan kungiyar Boko Haram.
Ya zuwa yanzu akwai ‘yan mata da suka kai 112 da suka rage a hannun ‘yan ta’addan ba tare da sanin makomarsu ba.
Mrs. Rebecca Samuel mahaifiyar daya a cikin ‘yan matan da suka rage hannun ‘yan Boko Haram ta yi kira ga shugaban kasa da ya kara azama a kokarin kubutar da ‘yan matan.
Ta kara da cewa tana sane da kokarin da hukumomin gwamnati ke yi a kan wannan batu akwai bukatar kara kaimi.
Rebecca ta ce tana fuskantar kunci a rayuwarta da yawan tunani na rashin ‘yarta amma ta ce tana addu’a duk lokacin da za ta shiga bacci.
Mrs. Rebecca Samuel ta yi wadannan kiraye kirayen ne a wata hira da ta yi wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Abuja, Sale Shehu Ashaka.
Hukumomin Najeriya dai a baya, sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarisu wajen ganin sun kubutar da 'yan matan da suka rage.
Ga cikakkiyar kuma hira da suka yin:
Your browser doesn’t support HTML5