Satar Danyen Mai A Nijeriya

Mayakan kungiyar "Niger Delta Vigilante Group" ta Ateke Tom su na rawar daji cikin sansaninsu

Tun ba yau ba ake cewa ana satar danyen mai a Nijeriya daga Neja Delta to sai dai yanzu lamarin ya yi kmari.
Yanzu dai satar dayan mai a Nijeriy ya yiwa kasar katutu lamarin ya yi tsami kamar barayin sun fi karfin gwamnatin kasar.

Yanzu a fili take cewa ana asarar kimanin gangar mai dubu dari hudu kowace rana ta Allah, wato sau talatin a wata ko kuma sau dari uku da sitting da biyar kowace shekara. Gwamnatin kasar ta ce tana asarar fiye da dala miliyan daya kowace rana da lalata bututun mai da ma wasu kayan aikin fitar da man.

A wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan Neja Delta Kingsley Koko ya ce kawo yanzu alkaluma da aka fitar kan satar danyen mai yace cikin wata uku kasar ta yi asarar kashi goma sha bakwai cikin dari da man da ake fitarwa. Ya kara da cewa kasar na asarar kudi kimanin dala miliyan shida duk shekara ko kuma nera miliyan dari tara da sittin.Wani babban batu da ke yin sarkakiya a harkokin man kasar kuma shi ne katutun cin hanci da rashawa ya addabi fannin na mai da kuma rufa-rufa da ake yi dangane da yarjejeniyar dake tsakanin gwamnatin Nijeriya da kuma kasashen waje.

Shi kansa yankin na Neja Delta na cigaba da gurbacewa sakamakon aikin hakar mai yayin da al'umomin yankin ke kukan ana mayardasu saniyar ware. Halin da ake ciki yanzu matasan yankin na cigaba da fasa bututayen mai tare da satarsa.

Rundunar tsaro ta JTF ta dade tana tsaron aikin mai a yankin to sai dai yadda matsan ke samun nasarar aiwatar da satar man ya sa rundunar bata yi tasiri kamar yadda aka nufa ba. Kwamando Kabiru Aliyu shi ne kakakin rundunar kuma ya ce shugaban kasa ya ba kwamandansu umurnin cewa ya tabbatar an dena satar danyen mai da ake yi. Sun je cikin lungu lungu da ake kulla satar an samu jirage guda goma sha bakwai. Cikinsu uku basu da takardu kuma an kamasu. An kuma kama mutane da yawa da suke ta'asar. An kuma kona wararen da suke fakewa suna satar.

Ga rahoton Lamido Abubakar.

Your browser doesn’t support HTML5

Satar Danyen Mai A Nijeriya-3.20