Satar Bayanai Ta Kafar Whatsapp

Whatsapp

Bincike ya nuna masu kutse ta duniyar gizo da kafofin sadarwa na satar bayanan mutane ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta WhatsApp, wajen nadar muhimman bayanan bankin mutane.

Masu kutsen dai na amfani da wata dabara ta aikawa mutane sakon karta kwana wanda ke dauke da wata boyayyiyar manhaja, wanda da zarar mutum ya bude sakon manhajar zata binciki na’urar da kuma nade muhaimman bayanai.

Yanzu haka dai masu kutsen na amfani da wannan hanyar ne kadai a dandalin WhatsApp wajen satar bayanai, a kasar Indiya da sauran wasu kasashe. Masu kutsen na aikawa da sakonnin ne da sunan makarantar koyan harkokin tsaro ta kasar Indiya, ko kuma hukumar bincike laifuka ta Indiya.

Hanyar da mutane zasu iya kare kansu da muhimman bayanansu shine idan suka sami sako daga wani wanda basu sani ba kar su bude, su kuma rufe shi ta hayar da ba zasu ‘kara samun sakon ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Satar Bayanai Ta Kafar Whatsapp - 1'05"