Kwallon Kafa Ta Saci Bindigogi A Ofishin 'Yan Sanda

Sanadiyar kallon wasan kwallon kafa ya jawo wasu barayi suka shiga ofishin 'yan sanda a kasar Kenya inda suka yi awon gaba da bindigogi, da kunshin alburusai guda uku, da kuma jakar alburusai.

Lamarin ya faru ne a ofishin ‘yan sanda dake kauyen Kobujoi a gundumar Nandy dake kasar Kenya, a yayinda 'yan sandan suka tafi kallon wasan kwallon kafa na majigi wanda aka buga ranar talatar da ta gabata tsakanin kungiyoyin Manchester United da Barcelona da kuma Ajax da Juventus na gasar zakarun Turai wato UEFA Champion's League na bana.

'Yan sandan sun gano hakanne bayan da aka tashi daga wasan yayinda suka koma bakin aikin nasu sai suka tarar da satar da barayin sukayi inda suka gano cewar bakin akwatin ajiye makaman a bude, nan da nan suka dukufa binciken ta yaya barayin suka shiga.

Tuni dai shugaban 'yan sanda na gundumar ya kai ziyara ofishin 'yan sandan da abun ya faru domin ganewa idonsa yadda lamarin ya faru.

A yanzu haka dai bincike yayi nisa na ganin an samo makaman da aka sace, sannan kuma a hukunta barayin da ake zargin sun yi satar.

Kwamishinan 'yan sandan mai suna Samuel Kimiti ya bada tabbacin faruwar lamarin, inda ya kara da cewar suma 'yan sandan da abun ya faru a ofishinsu a na cigaba da binciken su kan afkuwar lamarin.