Sashin Arewa - Maso Gabas Ke Da Kashi 65.2% Na Ciwon Inna

Yaki da Cutar Shan Inna a Najeriya

Hukumar Lafiya ta duniya (WHO) tace kashi sittin da biyar da digo biyu na masu fama da ciwon shan inna suna sashin arewa maso gabashin Nigeriya.
Hukumar Lafiya ta duniya (WHO) tace kashi sittin da biyar da digo biyu na masu fama da ciwon shan inna suna sashin arewa maso gabashin Nigeriya.

Kodinaton hukumar na jihar Bauchi, Dr Adamu Ningi ne ya fadi haka a tattaunawa da yayi da manema labarai a Bauchi. Ya bayyana damuwarsa cewa shigowar masu gudun hijira daga jihohi kamarsu Plateau, Borno da Yobe, domin matsalar rashin tsaro zai iya sa a sami bullar cutar a jihar Bauchi.

Dr.Ningi ya bayyana cewa Hukumar Lafiya ta duniya ta kafa wuraren shan magani a kan iyakoki domin yin rigakafi ga yara kasa da shekara biyar, kamin shiga jihar. Ya kuma ce sun kafa wuraren shan magani a kauyuka cikin jihar dake kusa da iyaka domin kare al’ummar jihar da kuma masu shigowa daga kamuwa da kuma yada cutar. Haka kuma ana yin allurar rigakafi a ga mutane dake zaune ko kuma shigowa a kan iyakokin jihar.