Sarkin Spain na Shida, Felipe ya yi Allah wadai da hukumomin Catalan, yana mi cewa sun take doka, bayan da suka gudanar da zaben raba gardama a ranar Lahadin da ta gabata.
A wani jawabi da yi a jiya Talata,wanda aka watsa a kafafen talbijin, basaraken, ya yi kiran hadin kai, yayin da dubban ‘yan kasar suka bazama akan tituna a arewa maso gabashin Lardin kasar, suna zanga zangar nuna adawa kan matakan da ‘yan sanda suka dauka na far ma wadanda suka fita yin zaben.
Shugabannin ‘yan aware a yankin na Catalonia, sun sha alwashin za su ayyana yankinsu a matsayi mai cin gashin kansa, duk da cewa hukumomin Madrid sun bayyana zaben a matsayin haramtacce.
Shugaban Catalan, Carles Puigdemont (kales pujdimond) ya fadawa BBC cewa ayyana ballewar yankin daga kasar ta Spain zai zo nan da wasu kwanaki masu zuwa.
Kungiyoyin kwadago a bangaren Catalonia, sun yi kiran da a gudanar da yajin aikin gama gari, domin nuna fushi kan yadda ‘yan sanda suka wulakanta mutanen da suka fita yin zaben