Sarki Sanusi Ya Gargadi 'Yan Siyasa Su Guji Sa Matasa Abunda Ba Zasu Sa 'Yayansu Ba.

Mai Martaba Sarkin Kano Lamido Sanusi II

A dai wajen gagarumin taron nadin sarautar sarkin matasan Adamawa,mai martaba Sarkinn Kano Mallam Muhammadu Sanusi II ya fasa kwai ne inda ya ce abun takaici ne ake maida matasa dake zama karnukan farautar yan siyasa.

Da farko sai da Sarkin Kano Lamido Sanusi II ya soma da yabawa masarautar Adamawa da kirkiro da sarautar sarkin matasa da yace zai taimaka wajen fadakar da matasa halin da kasa ke ciki,ko kuma wajen gangamin wayar da kan matasa kan wani batu dake damun al’umma.

Sarkin na Kano ya gargadi matasan Adamawa da ma na Najeriya gaba daya kada su yadda 'yan siyasa su yi anfani dasu 'yan bangar siyasa. Ya ce kafin su yadda duk dan siyasan da ya neme su da zama 'yan banga, su gaya masa ya fara da 'ya'yansa da 'ya'yan 'yanuwansa. Ya ce ba daidai ba ne su bari ana mayar dasu karnukan farauta a lokacin zabe.

A kullum dai gwamnatocin jihohi kan yi tutiyar cewa suna nasu kokari, kamar yadda Gwamnan jihar Adamawa Senata Muhammadu Bindow Jibrilla ya bayyana a wannan taro.

Mai martaba Lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, ganin cewa shine uban biki ya nuna farin cikinsa, musamman da kalamun Sarki Lamido Sanusi II.

Wakili Boya dai shine Sarkin Matasa na biyu tun kirkiro sarautar a Adamawa,kuma nadin nasa ya biyo bayan tube tsohon sarkin matasan farko ne Senata Abdul’Aziz Murtala Nyako,wanda Lamidon Adamawan ya tube a watannin baya shi da mahaifinsa kuma tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako dake zama tsohon sarkin yamman Adamawa.

Kamar yadda aka saba fitaccen mawakan Fulani na ciki da wajen Najeriya ba’a barsu a bay aba.

Ga rahoton Ibrahim Abduaziz da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Sarkin Kano YA Ja Kunnuwan Matasa Akan Zama 'Yan Bangan Siyasa - 3' 17"