Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya amince da nadin da gwamnatin jihar ta masa na mukamin shugaban Majalisar Masarautun Kano, Kwamishinan Yada Labarai, Muhammed Garba ya fadawa Muryar Amurka.
Wannan sanarwa na zuwa ne bayan da rahotanni suka yi nuni da cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Sarki Sanusi, wa'adin kwana biyu ya ba da amsa kan nadin da aka masa.
“Alhamdulillah, Mai Martaba Sarki da gaggawa ya dawo da amsa cewa ya amince ya karbi wannan nadi da aka masa.” Garba ya fadawa Muryar Amurka a yau Juma’a, a wata hira da ya yi da Aishatu Sule.
Ya kara da cewa, "na tabbatar da cewa, in Allah ya yarda, wannan amince wa da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi ya yi, na ya jagoranci wannan majalisa ta Sarakuna, na tabbatar da zai kawo saukin ka-ce-na-ce da ake ta yi."
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne, gwamantin jihar ta Kano ta nada Sarki Sanusi a wannan mukami, ta kuma umurce shi da ya kira taron kaddamar da majalisar "ba da bata lokaci ba."
Sai dai fadar gwamnatin kamar yadda Garba ya fada wa VOA, ta aika wa da Sarki Sanusi wata wasika ta neman karin haske, domin Sarkin bai ba da cikakkiyar amsa kan nadin ba.
“Wasika ta farko da aka aika, kusan amsar da aka bayar, ba ta nuna cewa an amince da wannan nadi ko ba a yi ba, shi ya sa mai girma gwamna ya sake ba da umurni na cewa, a sake rubutawa mai martaba Sarki, ya fada cewa ya amince ko bai amince ba.”
Kamar yadda kuma rahotanni suka nuna, gwamnatin ta ba Sarki Sanusi wa’adin kwana biyu ya fadi matsayarsa kan nadin.
Batun amincewa da wannan nadi, shi ne mataki na baya-bayan nan da takaddamar kirkirar sabbin masarautu ta kai.
Gwamnatin jihar ta Kano ta kirkiri wasu karin kishiyoyin masarautu hudu, matakin da wasu dama ke ganin yunkuri ne na rage karfin ikon Sarki Sanusi, wanda rahotanni ke nuna cewa yana yawan sukar lamirin gwamnatin Ganduje.
Saurari cikakkiyar hirar Aishatu Sule da Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Muhammed Garba:
Your browser doesn’t support HTML5