Kamar ko wace kasa, Faransawa na neman sauyi a harkokin su na yau da kullum, sai dai kuma da yawansu sun guji mai ra'ayin rikau, wato ‘yar takara Marine Le Pen, wadda ke cewa za ta fidda kasar ta Faransa daga cikin kungiyar tarayyar turai.
Amma abokin hamayyarta mai matsakaicin ra'ayi, Emmanuel Macron, wanda sabo ne a harkokin siyasar kasar ta Faransa, shi mutane suka fi raja'a a kansa, sai dai shi kuma wasu na masa kallon tamkar wakilin mutanen zamani ne.
Ita dai Marine Le Pen,ta sake tsara jamiyyar ta ce na National Front bayan ta karbi ragamar jam'iyyar daga mahaifinta, wanda wasu daga cikin manufofin ta ya janyo mata mabiya sosai.
Sai dai kuma ‘yan kasar na nuna damuwarsu daga yi yuwar ficewar kasar ta Faransa daga kungiyar tarayyar Turai wanda hakan na iya zame mata cikas musammam dangane da batun kudinta na bai daya.