Sarakunar Gargajiya a Jamhuriyar NIjer Sun Gana Da UNICEF

Shugaban kasar Nijer

Sarakunar gargajiya na jamhuriyar Nijar sun gudanar da wata ganawa da reshen hukumar tallafawa yara UNICEF a jamhuriyar Nijar, inda bangarorin guda biyu suka yi bitar yarjejeniyar da ke tsakanin su kamar yanda mai martaba sarkin Dogarawa Alhaji Ibrahim Attawel yayi ma manema labarai cikaken bayyani.

Yarjejeniyar bangarorin biyu ta samo asali ne kimanin shekaru biyar da suka wuce, wacce aka kulla ta a kan wayar da al’umma a kan al’adu da gargajiya da suke kawo koma baya ga ci gaban rayuwar jama’a. Zaman ta su ta tattauna a kan muhimmancin karatun yaran mata.

Sarakunar sun yi dubi a kan batun aurar da yaran mata masu karancin shekaru wanda hakan na kawo tsaiko ga karatunsu. Mai Magana da yawun sarakunar yace akwai wayar ta musamman da suke baiwa iyaye idan suna niyar aurar da yayansu tun suna kanana.

Sai dai yace al’amura sun fara sakewa kuma hakan na tabbatar da mutane na fahimtar nasihar da sarakuna da shugabannin jama’a ke yi musu.

Your browser doesn’t support HTML5

Niger Chiefs