Sarakunar Adamawa Suna Fadakar da Al’ummarsu a Kan Zabe

Fadar Lamidon Adamawa Dr Mustapha Barkindo

Sarakunar gargajiya a jihar Adamawa sun fara fadakar da al’ummarsu game da zuwa yin rajista don samun daman yin zabe a shekarar 2019. Wannan fadakarwar tana zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zabe ta INEC take kara wa’adin sabunta katin zabe.

Sarakunar gargajiyar na jihar sun kuma yi kira ga hukumar zabe ta INEC tayi kara runfunan zabe a jihar ganin cewar duk da Karin wa’adin da hukumar zaben tayi na rajistan masu zabe, wasu mutane a jihar basu san da wannan aikin ba.

Sarakunar gargajiyan sun gargadi al’ummarsu da su fita su je su rubuta sunayensu wanda hakan ne zai basu daman kada kuri’a a zabuka masu zuwa. Alh.Muhammadu Inuwa Baba Paris ,Dan Isan Adamawa kuma hakimin Jimeta dake zama cibiyar kasuwancin jahar, yace Lamidon Adamawa Dokta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa shine ya umarce su da su tashi haikan wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin samun katin zaben, inda yace yanzu haka suna bukatar Karin cibiyoyin karbar katunan.

A nata bangaren, hukumar zaben ta INEC,ta sha alwashin duba wannan batu. Barr.Kassim Gaidam dake zama kwamishinan zabe a jihar, yace suna sane da matsalar, kana kuma yace aikin sabunta katin zabe na tafiya babu kama hannun yaro.

Your browser doesn’t support HTML5

ADAMAWA