Shugabannin sun nuna fargabar su da karuwar tashe tashen hankula na hare haren yan ta'adda musanman a yankin Arewacin Najeriya, da kuma yankin kudu maso gabashin kasar da yanzu yake neman tsallakowa zuwa yankin yammancin Najeriya, bisa la'akari da harin yan bindiga a cocin katolika dake garin Owo ta jihar Ondo da ya haddasa hasarar rayukan fiye da mutane 40.
A cewar Basaraken Yarbawa Oba Oluwa na kuta, a jihar Osun Alhaji Hammed Adekunle Makama da yayi magana a madadin sauran Oban na yankin yarbawa, ya ce suna sane da kokarin da jami'an tsaron kasa musanman sojoji da yan sanda ke yi na tabbatar da doka da Oda, don haka akwai bukatar gwamnati ta kara azama wajen samar da kayan yaki da kuma inganta jin dadin dakarun kasar dake fagen daga.
Haka kuma basaraken ya yi amfani da damar wajen watsi da zargin da wasu yan kasar ke yi wa tsohon hafsan sojin kasar General Tukur Burutai na sama, da fadi da kudin sayen makamai ,duk kuwa da cewa hukumar ICPC ta wanke General Buratai daga duk wani laifi, ya kuma ce ire-iren wannan zargi na zubar da darajar kasar a idon duniya.
Shima shugaban wata kungiyar yan Arewacin Najeriya mazauna lagos, Alhaji Ado Shuaibu Dan Sudu, ya baiyana goyon bayan sa ne ga matakin gwamnan jihar Zamfara na neman al'umar yankin da yan bindiga suka gallaba da su dauki makamai domin kare kansu, inda ya ce daukan matakin kare kai shine mafita kuma suna goyon bayan gwamnan jihar Zamfara akan wannan mataki domin yanzu akwai alamun gwamnatin tarayya ta gaza.
A baya-bayan nan yan bindiga su ka halaka wasu jami'an tsaro ciki harda hafsoshi fiye da 10 da sace wasu yan kasar China mutum hudu, wadanda ke aikin hakar ma'adinai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger.
Yan Najeriya na ci gaba da yin kira ga mahukunta da su tashi tsaye wajen magance matsalar tsaro da ke addabar kasar, kamar dai yadda suke bada fifiko akan harkokin siyasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5